Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dauda Lawal: Ƙarairayi Da Ƙazafin Da Ruɗaɗɗun ‘Yan Siyasa Ke Yaɗa Wa

Daga Bala Idris, Gusau “Idan ka bincika da kyau a zagaye da shugaban ƙwarai, ko ka yi dubi ga halayensa, babu abin da za ka tara...Daga Bala Idris, Gusau

“Idan ka bincika da kyau a zagaye da shugaban ƙwarai, ko ka yi dubi ga halayensa, babu abin da za ka tarar sai ɗabi’a mai kyau.” Wannan wata maganar hikima ce wacce Brian Cooper ya yi, kuma ta yi daidai da irin rayuwar tsohon Babban Daraktan Bankin First Bank, Dr. Dauda Lawal.

Lokaci ya sake zagayo wa, ciwon hassadar mahassada kuma maƙiyan Dr. Dauda Lawal, waɗanda suka cika suka batse da muguwar farfagandar siyasa, kuma suka sha alwashin sai sun yaɗa wannan muguwar farfaganda ga al’ummar Nijeriya musamman ma ga mutanen Jihar Zamfara. 

Bayan sun gaza cimma muguwar manufarsu ta yaɗa ƙazafi, su ɓata suna, da tarwatsa mutunci da ƙimar da Dauda ya samarwa kansa a tsawon rayuwarsa na aikin banki. Yanzu ta ƙare musu, sun koma ƙirƙirar labarai daga hukuncin da Kotun Ƙolin Nijeriya ta yi.

A sabon salon rashin ɗa’a da suka zo da shi, waɗannan marasa ƙimar kuma gurɓatattun ‘yan siyasa sun yi amfani da wasu kafafen sadarwa inda suka ce wata ƙungiyar ƙarya ta goyi bayan gwamnatin tarayya da EFCC a ƙoƙarinsu na son bincikar badaƙalar dala 40 da ake zargin Dauda Lawal a kai.

Abin da ya fi ban takaici a nan shi ne yadda tsabar son rai da neman wurin zama ya sa wani gwamna ya ɗauki nauyin ƙirƙira tare da yaɗa wannan ƙarya, su kuma kafafen sadarwan suka gaza yin bincike don tabbatar da gaskiyar zancen ko akasin haka. 

A yadda suka yaɗa labarin, kana gani ka san mutane ne da zukatansu suke cike da ƙin Dr. Dauda Lawal.

 Ƙiyayyarsu gare shi da yaɗa ƙazafi ba abin damuwa ba ne, wane ne ma ya damu da ruɗewar gwamnan da bai san makomarsa ba? Kawai ana tankawa ne don a bayyana gaskiya kuma don kar a bari a ruɗar da ‘yan Nijeriya. 

Idan ban da hauka da ruɗewa irin ta waɗannan mutane, wane ne zai riƙa tambayar silar dukiyar mutumin da duniya ta sanshi a harkar banki kuma ya kai matakin Shugaba a Babban Banki irin First Bank? Mutumin nan fa, wato Dr. Dauda ya kwashe kusan shekara 30 yana aiki a banki, inda ake bincike da bibiyar yadda mutum ya tara dukiyarsa. Wannan kaɗai ya isa ya nuna jahilcin waɗannan mutanen.

Babu komai a cikin zarginsu sai ƙarya, ƙazafi, ƙoƙarin ɓata suna da neman a sansu. Sun manta cewa, wannan abin da suka yi, tamkar yin fito na fito ne da Kotun Ƙolin Nijeriya. 

Ga yadda lamarin ya kasance, don mutane su sani. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi hukunci wanda ke hani ga EFCC kan ƙwace Dala Miliyan 40 daga hannun Dr. Dauda Lawal, wannan hukuncin na Kotun Ɗaukaka Ƙara an yanke shi ne a shari’a mai lamba: CAILAG/CƁ/480/2019; DAUDA LAWAL v. EFCC & ANOR a ranar 25 ga watan Maris, 2020.

Don haka ne Hukumar EFCC ta ɗaukaka ƙara, wanda kuma Kotun Ƙoli ta Nijeriya ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar a ranar 12 ga watan Maris, 2021 a hukunci mai lamba SC/CR/21212020; EFCC v. DAUDA LAWAL.

Wannan hukunci na Kotun Ƙoli ya wanke tare da kulle duk wani zargi da ake yi wa Dr. Dauda Lawal. Kuma a ƙa’idar shari’a, wannan kes ɗin ya mutu har abada. Abin da ya ke nufi babu gamsassun hujjoji da ke nuna cewa Dr. Dauda ya samu kuɗaɗen ne ta hanyar da ba su dace ba. Hukunci ne aka yi shi a bayyane, kuma kowa na iya bincikawa don tabbatarwa matuƙar ba mutum na da wani mugun nufi ba ne.

Idan ba su sani ba, su sani yanzu. A gaban Kwamitin Salami wanda Shugaban Ƙasa ya kafa don bincikar Magu, Dauda Lawal ya bayyanawa kwamitin yadda tsigaggen Shugaban na EFCC ya yi ta nemansa da ya ba shi cin hanci don a kashe kes ɗin. Amma Dauda ya ƙi aminta da wannan buƙata, ya yi tsayin daka kan sai dai a ci gaba da shari’a har gaskiya ta yi halinta.

Babu irin cin mutunci, barazana da tursasawa da Dauda bai gani ba. Bayan da EFCC ta gaza kama shi da laifi sai aka yi amfani da Hukumar Kwastam. Inda jami’an hukumar suka je gidansa dake Kaduna da sunan binciken ko motocinsa na alfarma suna da cikakkun takardun lasisi. Sun yi binciken sun gama, amma sun kasa kama shi da laifi, gabaɗaya motocinsa suna da lasisi.

Shin mutane irin Dauda nawa muke da su a Nijeriya? Waɗanda za a sako gaba irin haka da bincike kuma su fito sumul ba tare da laifi ba. Wannan fa mutum ne da bai taɓa yin aikin gwamnati ba, a ƙa’idar aikinsa, ba dole ba ne sai ya bayyana ƙadarorinsa da dukiyarsa.

Dole ne waɗannan ruɗaɗɗen ‘yan siyasar kuma maƙiyan ganin ci gaban Jihar Zamfara su daina wannan farfaganda ta tsantsan ƙiyayya. Su burinsu sai sun ɓata sunan Dauda, sai sun ruguzo da martabarshi da ƙimarshi kamar yadda jama’a ke kallonsu.

Ya zama tilas mutanen nan su sani cewa, su yi ta yaɗa ƙazafi da ɓatancinsu, wannan ba zai taɓa sauko da irin ƙima da sunan da Dauda Lawal ke samu a tsakanin mutanen Jihar Zamfara ba. Wannan ne ke ba su tsoro.

Bala ya rubuto ne daga Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara. 

No comments