DSS Na Neman Sunday Igboho Ruwa A Jallo

 


BBC Hausa ta labarto cewa; Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya wato DSS ta ce tana neman shugaban masu rajin kafa ƙasar Yarabawa Sunday Igboho ruwa a jallo.

Ta sanar da hakan ne kwana guda bayan wani sumame da ta kai gidansa inda ta gano tarin makamai da dama.

Mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya, ya ce suna buƙatar Sunday Igboho, domin dakile aniyarsa ta haifar da yamutsi a Najeriya.

An yi arangama tsakanin jami'an hukumar da masu gadin Igboho, har ta kai ga an kashe mutum biyu, a lokacin ne kuma ya tsere.

Post a Comment

0 Comments