Sama da mutane dubu 9 da dari 9 da 48 ne suka sanya hannu a takardar neman gwamnatin Nijeriya ta haramta cin naman kare da sayar da sh...
Sama
da mutane dubu 9 da dari 9 da 48 ne suka
sanya hannu a takardar neman gwamnatin Nijeriya ta haramta cin naman kare da sayar da shi a Nijeriya.
Ana
cin nama kare a kudu maso gabashin
Najeriya da Kudu maso kudanci da ma wasu sassan arewacin kasar.
A
shekarar da ta gabata ne wata mai rajin
kare hakin dabbobi da ke zaune a Birtaniya, Natasha Choolun ta fara wannan
fafutuka ta kafar intanet, amma lamarin ya samu karbuwa ne a Alhamis din da ta gabata, inda ‘yan Najeriya
da dama suka shiga fafutukar, tare da sanya hannu a takardar korafin.
Choolun
ta ce kasuwar naman kare na ci a Nijeriya, inda karnuka ma ba sa isa, har ya
kai ga ana shigowa da su daga Nijar, inda ta ce wanna ya jefa karnuka cikin
hadarin shudewa.
No comments