Duk Da Hukuncin Kotu APC Ta Ce Za Ta Gudanar Da Taronta Na Ƙasa


Jam'iyyar APC da ke mulki a Nijeriya ta ce za ta gudanar da taronta na ƙasa kamar yada ta tsara a ranar Asabar mai zuwa, 31 ga watan Yuli 2021.

A wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakatarenta na ƙasa a kwamitin shirya taron, Sanata John James Akpanudoehe, APC ta ce tuni kwamitin da ta naɗa domin tsare-tsare da sa ido kan yada taron zai kasance suka dukufa aiki.

Ta ce ta fitar da sanarwa ne domin jan hankalin mutane kan ra'ayoyin da wasu ƴaƴan jami'iyya da damuwar da suke nuna wa gabannin taron.

Sanarwar ta kuma ce hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaɓen gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ba shi da alaƙa da taronta.

Post a Comment

0 Comments