A kalla mutum 30 ne jami'an hukumar EFCC suka kama a yayin wani samame a Otel din Parktonian a unguwar Lekki ta jihar Legas. A lokac...
A kalla
mutum 30 ne jami'an hukumar EFCC suka kama a yayin wani samame a Otel din
Parktonian a unguwar Lekki ta jihar Legas.
A
lokacin samamen na ranar Talata, jami'an EFCC sun samu shiga dakunan wadanda
ake zargin ne ta hanyar kwace makullan dakunansu daga jami'an otel din da
karfin tsiya.
Jaridar
Punch ta ruwaito cewa EFCC ta bayyana cewa an kama mutanen ne bisa zargin
aikata zamba ta intanet.
EFCC
ta ce ta samu bayanan siri da suka tabbatar mata da cewa otel din ya zama
matattarar masu aikata zamba da yaudara ta intanet, shi ya sa ta aika
jami'anta.
No comments