Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Maqari Zai Maka Shaikh Gadon Kaya A Kotu Bisa ‘Kazafin’ Da Ya Yi Masa

  Daga Muhammad A. Dalhatu Daya daga cikin Limaman Masallacin Juma’a na babban birnin Tarayya Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana cewa ...

 


Daga Muhammad A. Dalhatu

Daya daga cikin Limaman Masallacin Juma’a na babban birnin Tarayya Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya maka Shehin Malamin nan dake Kano, Sheikh Abdullahi Gadon Kaya bisa zarginsa da yi masa kazafi da yunkurin  bata masa suna kan batun Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara. 

A wani bidiyo da MADOGARA ta kalla, Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyanawa Gadon Kaya sharuddan janye zargin da ya yi masa a wata hudubar ranar Juma’a da Sheikh Gadon Kaya din ya gabatar wanda hakan ya janyo cece-kuce a tsakanin al’ummar Musulmi a Nijeriya.  

Gadon-Kaya ya zargi Limamin na Abuja da yi wa al’ummar  Musulmi zagon kasa domin bai wa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara kariya. Inda ya tabbatar da cewa yana da wasu bayanai cikin ‘audio’na Farfesa Maqari da yake kira a waya yana tattaunawa domin yi wa Musulmi zagon kaya. 

Farfesa Maqari da almajiransa sun nemi da Sheikh Gadon Kaya ya fito da bayanan da ya ce yana da su cikin ‘audio’, wanda suka ce idan ya gaza hakan, za su maka shi a kotu bisa wannan zargin.  


No comments