Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Moghalu Ya Taya Sarki Sanusi Murna Cika Shekara 60 A Duniya

Tsohon dan takarar Shugaban Kasa a zaben shekarar 2019, kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Farfesa Kingsley ...Tsohon dan takarar Shugaban Kasa a zaben shekarar 2019, kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Farfesa Kingsley Moghalu ya taya tsohon Sarkin Kano kuma Khalifan Darikar Tijjaniyya, Mallam Muhammadu Sanusi II murnar cika shekara 60 a duniya.

A yau 31 ga watan Yuli ne Muhammadu Sanusi II ke cika shekara 60 da haihuwa; Moghalu a wata takardar taya murna wacce ya rattabawa hannu kuma aka rabawa manema labarai yau a Abuja, ya ayyana Khalifan na Tijjaniyya a matsayin shugaba na gari.

Ga cikakkiyar sanarwar taya murnar:

"Ina taya ka murna bisa cika shekara 60 da ka yi a yau, tare da yin godiya ga Ubangiji mahalicci. Barka da zagayowar ranar haihuwa! Ina roƙon Allah Ya ja kwananka.

"Yayin da ka ke cika shekara 60, za a ci gaba da tuna irin muhimmiyar rawar da ka taka wurin bunƙasar tattalin arzikin Ƙasa mafi girma a Nahiyar Afirka, lokacin da ka riƙe muƙamin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya daga shekarar 2009 zuwa 2014; gudummawarka ga sha’anin ƙasa, da wanda ka bayar ga ɓangaren addinin Musulunci da harkokin al’umma. Haka nan a matsayinka na marubuci kuma fasihin masani wanda ya shahara a faɗin duniya.

"Ba kawai girmamawar da ka samu a matsayin gwarzon Gwamnan Babban Banki na duniya ba, ka kasance gwarzon Gwamnan Babban Banki a Nahiyar Afirka a shekarar 2012, wanda mujallar ‘The Banker Magazine’ ta baka – daɗin daɗawa a shekarar 2011 Mujallar TIME ta sanya ka cikin jerin mutum 100 masu tasiri a duniya.

"Ina matuƙar alfahari da kai, ina shauƙin kiranka da ɗan uwa kuma abokina, ina alfahari da muhimmin aikin da muka yi tare – sauya tsarin gudanarwa na harkar banki ya yi daidai da zamani da kuma irin tagomashin da Babban Bankin Nijeriya ya samu a ƙarƙashin jagorancinka. Waɗannan gyararrakin da muka samar cike suke da hangen nesa, jajircewa da kuma tattali da tsari kamar yadda ta tabbata bayan an samu mafita daga taɓarɓarewar tattalin arzikin da aka faɗa kafin zuwanka.  

"Ina tunawa cike da dubun godiya ga irin rawar da ka taka a bunƙasar rayuwata. Kai ne ka gayyace ni na dawo Nijeriya daga Geneva ta Kasar Switzerland a shekarar 2009, ka kuma shawarci Marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’adua kan a bani babban aikin Mataimakin Gwamnan Babban Banki domin na taimaka maka, inda na jagoranci sashen da ke sa ido kan tabbatar da tsarin daidaituwar kuɗi  ‘Financial System Stability (FSS)’.

"Tsayin daka da girmama tsarin shugabanci da muhimmanta hazaƙa a yayin hidimtawa ƙasa wani abu ne da ya sa nake girmamaka. Bayan dawowa ta gida, mun sauya daga abokan aiki zuwa aminai na har abada.

"Tasirinka da muhimmanci a bayyane suke a zamaninka na Sarkin Kano, da yanzu a matsayinka na Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya a Nijeriya.

Ina da tabbacin cewa za ka yi amfani da ƙwarewa ta shugabanci da ka ke da ita a wannan hidima ga addini don ganin yankin Arewacin Nijeriya ya bunƙasa ta dukkan fannoni.

"Allah Ya yi maka tsawon rai, Khalifah. Kuma Allah Ya albarkace ka da Iyalanka."
 
Na ka,
Kingsley Moghalu

No comments