Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

FGC Otukpo Ta Yabawa Shugaban Jami'ar MAAUN Bisa Gudummawar Da Ya Ba Su

  Hukumar gudanar da Kwalejin gwamnatin Tarayya dake Otobi a Otukpo ta jihar Binuwe ta jinjinawa shugaban rukunin Jami'o'...

 

Hukumar gudanar da Kwalejin gwamnatin Tarayya dake Otobi a Otukpo ta jihar Binuwe ta jinjinawa shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa  Adamu Abubakar Gwarzo bisa gudummawar da ya bai wa Kwalejin wajen gina filin wasan 'Volleyball' da kuma kwallon kwando (Basketball) a makarantar. 


Jiinjinar ta zo ne a cikin takardar da shugaban Kwalejin Mr. G. O. Amudipe ya sanyawa hannu ya kuma aika ga shugaban Jami'ar MAAUN inda kuma aka rabawa manema labarai a Kano a ranar Lahadi. 

"a madadin hukumar gudanarwa da ma'aikata da dalibai da kuma al'ummar Otobi, na rubuta wannan takardar ne domin bayyana jindadinmu da godiyarmu bisa gudummawar da ka bamu wajen gina wuraren wasanni na 'Volleyball' da kwallon kwando (Basketball) a kwalejin", inji takardar. 

Ya ci gaba da cewa; "babban gudummawarku ya taimakawa Kwalejin wajen bai wa masu neman ilimi a cikinta dama tare da taimakawa sauran al'ummar dake zagaye da kwalejin damar shagali", ya lurantar. 

"Kalmomi sun yi kadan wajen bayyana gudummawarka gare mu, na ji dadi bisa karamcinka", ya jaddada. 


Shugaban makarantar har wala yau, ya yi fatan cewa alkawarin naira miliyan daya da shugaban Jami'ar ta MAAUN ya yi a yayin kaddamar da ayyukan zai taimakawa kwalejin wajen siyan kayayyakin wasannin da ya kamata. 


A karshe shugaban makarantar ya tabbatar da cewa kwalejin za ta yi amfani da kayan aikin da kyau wajen domin biyan bukatar dalilan da ya sanya aka samar da su. 

No comments