Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gobe Za A Yanke Hukunci A Kan Shari'ar Shaikh Zakzaky

  Harkar Musulunci  a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta tabbatar da cewa a gobe Laraba ne babbar Kotun da ke jihar ...

 


Harkar Musulunci  a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta tabbatar da cewa a gobe Laraba ne babbar Kotun da ke jihar Kaduna, wadda Mai Shari'a Gideon Kurada yake jagoranta za ta yanke hukunci a kan shari'ar da ake wa jagoransu Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim wadanda ke fuskantar kallafaffiyar Shari'a tsawon shekaru hudu da suka gabata.

Wannan bayani yana kunshe ne a cikin Takardar Sanarwar Manema Labarai wadda Shugaban Dandalin Yada Labarai na Harkar Musulunci a Nijeriya, Malam Ibrahim Musa ya sanya wa hannu, ya kuma raba ta ga Manema Labarai a yau Talata”.

Shugaban Dandalin Yada Labaran ya ce Kotun za ta yanke hukunci a kan bukatar korar Shari'ar ne, kamar yadda Mai jagorantar Lauyoyin Shaikh Zakzaky, Mista Femi Falana SAN ya bukata, a inda ya bayyana cewa duk da wadanda suka shigar da kara sun gabatar da shaidu goma sha biyar (15), to amma babu daya daga cikin su wanda ya iya danganta laifuka da ake tuhumar aikatawa da Shaikh Zakzaky.

A zama na karshe wanda Kotun ta gudanar a ranar 01/07/2021, jagoran Lauyoyin da ke kare Shaikh Zakzaky, Femi Falana SAN ya roki Kotu ta yanke hukunci na wanke wadanda suke karewa daga aikata laifi, kuma idan haka ya wakana, to Shaikh Ibraheem Zakzaky da mai dakin sa Malama Zeenah Ibrahim za a sake su daga kamawa da tsarewa da ake yi masu tun cikin watan Disambar 2015.

Idan za a tuna, wadansu Kotuna guda biyu tuni suka yanke wannan hukuncin korar kara da Kuma wanke wa fes daga tuhumar aikata laifi ga kusan kimanin 'yan uwa Musulmi na Harkar Musulunci a Nijeriya 200 wadanda aka tuhuma da aikata laifuka iri daya da wadanda ake tukumar Shaikh Zakzaky da aikatawa.

Haka zalika, a shekarar 2016 babbar Kotu a Abuja ta tabbatar wa da Shaikh Zakzaky da mai dakin sa Malama Zeenah hakkin su da 'yancin su na dan Adam, ta kuma bayar da Umarnin sakin su, amma abin kunya da mamaki sai gwamnatin tarayya ta kekashe kasa ta yi mursisi ta ki bin wannan umarnin Kotu na Sakin Shaikh Zakzaky da mai dakin sa Malama Zeenah Ibrahim.


No comments