Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin rusa wata unguwa da ke wajen babban birnin jihar nan take. Aliyu Sidi Lamido wa...
Gwamnan
Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin rusa wata unguwa da ke wajen
babban birnin jihar nan take.
Aliyu
Sidi Lamido wanda shi ne mai bai wa gwamnan shawara kan tsara birane, ya shaida
wa BBC Hausa cewa matakin ya biyo bayan ƙaurin sunan da unguwar da ake kira
Raymond Village ta yi.
Ya ce
unguwar ta zama matattarar "yan fashi da masu safarar miyagun ƙwayoyi da
safarar ɗan Adam da harkokin baɗala.
Gwamnan
ya ba da umarnin ne bayan wata ziyarar ba-zata da ya kai unguwar ranar Talata
tare da rakiyar shugabannin hukumomin tsaro.
No comments