Gwamnatin Buhari Ta Gaza Samar Da Tsaro -Bishop Kukah

 


Kafar watsa labarai ta RFI Hausa ta labarto cewa; daya daga cikin Dattawan Nijeriya kuma shugaban mabiyar darikar Katolika a Sakkwato Bishop Mathew Hassan Kukah ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza samar wa ‘yan Nijeriya tsaron da suke bukata kamar yadda ta yi alkawari kafin ta hau karagar mulki.

Yayin da yake gabatar da jawabi ga wani taro da ya kunshi ‘yan majalisun Amurka ta faifan bidiyo akan matsalolin tsaron da suka addabi Nijeriya, Kukah ya ce yaki da matsalar tsaro na daya daga cikin alkawuran da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa ‘yan Nijeriya kafin zaben shekarar 2015, amma har ya zuwa wannan lokaci babu wani abin kirki da suka gani dangane da kare lafiyar su.

Shugaban mabiya darikar Katolikan ya kuma zargi shugaban kasa Buhari da nada ‘yan kabilarsa da addininsa da yawa akan mukaman gwamnati sabanin yadda aka saba gani.

Kukah ya ce ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane yau sun mamaye yankin arewacin kasar da kuma sassan Nijeriya inda suke kai hari kan al’umma lokacin da suke so, abin da ke nuna gwamnatin ko ta gaza ko kuma bata damu da halin da jama’ar kasar ke ciki ba wajen murkushe wadannan mutane.

Shugaban mabiya darikar Katolikan ya ce abin takaicin shi ne shugaban kasa ya mayar da hankali kan bin tafarkin nuna banbancin wajen fifita bukatun mabiya addinin sa maza da mata.

Jaridar Daily Trust ta ce Kukah ya bayyana cewar a karon farko a tarihin Nijeriya, shugabannin bangarorin gwamnatin kasar da suka hada da shugaban kasa da shugaban Majalisar Dattawa da na Wakilai da Shugaban Kotun Koli dukkan su Musulmai ne.

Ya kara da cewar duk da yake wadannan shugabannin mutane ne masu kima, gasa tsakanin Musulmai da Kiristoci ya dada tabarbarewa irin yadda ba’a taba gani ba.

Shugaban mabiya darikar Katolikan yace labarin Leah Sharibu da kungiyar boko haram ta sace na nunawa karara kan irin yanayin da jama’a suka samu kan su da kuma addinin su.

Kukah ya ce a shekarar 2020 an kashe wasu daga cikin limaman su a arewa, yayin da masu tsatsauran ra’ayi na kama ‘yayan su da karfi suna Musuluntar da su, duk da cewa dimokiradiya ake gudanarwa a kasar ba tare da hukumomi masu karfi ba.

Shugaban ya ce suna bukatar taimako a bayyane wanda zai taimaka musu da ‘yayan su.


Post a Comment

0 Comments