Gwamnonin PDP Na Taro Kan Halin Da Najeriya Ke Ciki A Bauchi

 


Gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya na taro a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar

Gwamnonin 13 suna taron ne don tattaunawa kan halin da kasar ke ciki a yanzu haka da kuma na jihohinsu.

Batutuwan da suka shafi rashin aikin yi da yanayin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki da halin da dimokradiyya ke ciki kamar batun sauya dokokin zabe da na kundin tsarin mulki ne manya da za su mamaye taron na yay.

Sannan a yayin taron gwamnonin za su tuhumi gwamnatun tarayya kan yadda take tunkarar matsalar tsaro.

Kazalika za su bijiro da matakan da suke ganin za a bi a warware matsalolin.

Gwamnonin na PDP za kuma su karbi rahotanni daga wasu kwamitocin da ke aiki kan yadda za a yi wa jam'iyyar garambawul.

-BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments