Kasar Haiti ta nemi taimakon Amurka da Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin dakarunsu sun tsare mata wurare masu muhimmaci da suka hada da ...
Kasar
Haiti ta nemi taimakon Amurka da Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin dakarunsu
sun tsare mata wurare masu muhimmaci da suka hada da tashoshin jiragen ruwanta
da na sama, bayan kisan gillar da aka yi wa shugaban kasar Jovenel Moise.
Tuni
Amurka ta ce za ta tura jami’an FBI da wasu zuwa Port-au-Prince, kwanaki biyu
bayan kisan shugaba Moise a gidansa.
Da
yake tabbatar da bukatar, bayan ganawa da sakataren harkokin wajen Amurka da
wakilin Majalisar Dinkin Duniya, Ministan harkokin zaben Haiti Mathias Pierre,
yace suna fargabar akwai yiwuwar sojojin haya za su iya lalata wasu muhimman
wurara da kaddarorin gwamnati don sake haifar da rudani
Ma'aikatar
Harkokin Wajen Amurka da Pentagon duk sun tabbatar bukatar da Haiti tayi, na
taimakon tsaronta da kuma bincike kan kissan gillar, amma ba su fayyace ko za a
tura sojojin Amurka zuwa kasar ba.
Majalisar
Dinkin Duniya ba ta ba da amsa nan take kan bukatar da Haiti ba, amma wata majiyar diflomasiyya ta Majalisar
ta nuna akwai bukatar amincewar Kwamitin Tsaro kafin daukar mataki.
No comments