Daga Muhammad
A. Dalhatu
A yayin da mahajjata ke shirin
Ibadan hawar Arafat a yau Litinin, hukumomin Saudiya sun tabbatar da cewa babu
wani mani daga cikinsu da ya harbu da annobar korona, a daidai lokacin da kasar
ta samu sabbin mutane 12 da cutar ta kashe a ranar Lahadi wanda wannan
adadin ya haura adaddin wandanda cutar
ta kashe zuwa dubu 8,075 a fadin kasar.
Majiyarmu ta labarto cewa; ma’aikatar kiwon lafiyar
kasar Saudiya ta ce an samu sabbin mutane 1,055 da suka harbu da cutar cikin
sa’o’i ashirin da hudu da suka gabata, wanda ya haura jimillar adadin mutanen
suka harbu da cutar zuwa dubu 509,576 a kasar.
0 Comments