Haramta Kiwon Sake Ba Zai Yiwu Ba, Inji Gwamna Zulum


Bbc Hausa ta labarto cewa; Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ce matakin haramta kiwo sake a wasu jihohin ba zai yiwu ba.

A wani taro da ya gudana a Asaba babban birnin Delta, watanni biyu da suka gabata, gwamnonin kudu suka hada kai wajen daukar matakin haramta kiwon sake wanda suka ce shi ne musabbabin rikicin tsakanin makiyaya da manoma.

Sai dai wannan matakin nasu ya hadu da tsaiko inda gwamnatin tarayyar kasar ke cewa babu wanda ke da 'yancin hana wani yawo a fadin kasar.

Lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, zulum yace hana kiwon sake ba zai yiwu ba a wasu jihohin, har sai an shawo kan matsalar tsaro da kuma ta tattalin arziki.

"Sai mun fara kawo karshen rikicin siyasa da na matsalar tattalin arziki domin kullum karuwar talauci ake samu a yankunanmu wanda kuma hakan na kara tazzara matsalar tsaro."

"Akwai matsalar karanci abinci da ake mafa da shi a yankin arewaci saboda shi kanshi karancin abincin matsala ne don haka Borno ba ta neman a rika cewa aje noma sama da shekara biyu. ya kamata a ce ama barin manoma suna zuwa noma," in ji Zulum.

Post a Comment

0 Comments