Iyalan Shaikh Zakzaky Sun Jinjinawa Masu Muzahara, 'Yan Jarida, Lauyoyi Da Masu Rajin Kare Hakkin Dan AdamDaga Ammar M. Rajab 

Mohammed Ibraheem, Babban da a wurin Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Zakzaky, ya mika sakon godiyarsa ga masu muzahara, 'yan jarida, masu rajin kare hakkin Bil'adama, kungiyoyin fararen hula, da kuma tawagar Lauyoyin da suka kare mahaifinsa da dukkanin wadanda suka tsaya kyam wajen nuna goyon bayansu tun bayan kama iyayensa a shekarar 2015. 

A cewar sanarwar da Mohammed ya fitar da yammacin yau Alhamis 29 ga watan Yulin 2021, ya bayyana cewa; "kamar yadda kuka sani, a jiya mahaifina Sheikh Ibraheem Zakzaky da mahaifiyata Zeenah Ibraheem suka samu 'yancinsu, bayan da babban kotun jihar Kaduna, ta wanke su tare da sakin su daga dukkanin tuhume-tuhume da gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar gaban kotun". 

Ya ci gaba da cewa; "bayan mika godiyarmu ga Allah ta'ala, muna mika sakon godiyarmu ga dukkanin wadanda suka tsaya mana a yayin wannan jarabawar da ta dauki kwanaki 2055 kusan shekara 6", ya labarta. 

"Ni da dukkanin iyalinmu muna mika sakon godiyarmu musamman ga maza, mata da kananan yara wadanda suka tsaya kyam wajen fuskantar rashin adalci, tare da fuskantar hatsarin rasa rai wajen neman adalci da kuma 'yanci gare su (iyayena), a nan cikin gida da kuma kasashen waje. Jinjina ta musamman ga jaruman da suka tsaya a kowacce rana a Abuja ba kakkautawa har na tsawon shekaru 5 suna muzaharori, babban sadaukarwa ce da ba kasafai ake jinta ba, kuma tabbas irinsa na farko a tarihin Nijeriya", ya tabbatar. 

"Ina mika sakon godiyarmu ga kungiyoyin kare hakkin bil'adama, wadanda suka ci gaba da taimakawa wajen bamu murya a wannan lokaci mai tsanani. Jinjina ta musamman ga Amnesty International (kungiyar kare hakkin bil'adama ta duniya), Human Rights Watch, musamman ma Islamic Human Rights Commission (Hukumar kare hakkin bil'adama ta Musulunci), wadanda suka tsaya kyam wajen ganin ta'addancin da aka aiwatar a Disambar 2015 ba a bizne shi ba", ya jinjina. 

"Muna yabawa da kokarin kafafen watsa labarai masu 'yanci da 'yan jaridar da suka sadaukarwa gaskiya wajen haskakata a yayin fuskantar takunkumi, barazana harma da hare-hare. Muna yaba muku bisa jajircewa da jarumtaka, kuma muna son yi muku godiya a dukkanin lokutan da kuka ƙi yarda ku kawar da idanunku daga zalunci, nuna wariya da sauran miyagun laifuffukan da ake aikatawa da sunan kasa", ya nusasshe. 

"Daga karshe, ina mika sakon godiya ga Kwararrun tawagar Lauyoyi masu amana a karkashin jagorancin Cif Femi Falana, SAN, wanda duk da irin mummunan kulli domin jinkirtawa, tare da kokarin kawo cikas ga tsarin shari'a, amma tawagar lauyoyin ta jajirce kuma daga karshe ta yi nasara. Za mu kasance masu godiya har abada saboda kokarin da kuka yi, ” inji sanarwar. 

Idan za ku iya tunawa a ranar Laraba ne, Shaikh Zakzaky da matarsa, Malama Zeenah Ibraheem, kotu a Kaduna ta sake su tare da wanke su daga dukkanin tuhume-tuhume guda takwas ciki harda na kisan kai da kuma na tarwatsa zaman lafiya.

Post a Comment

0 Comments