Jami'ar MAAUN Ta Rasa Ma'aikacinta, Ali DaudaShugaba kuma mu'assasin Jami'ar Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British University dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan daya daga cikin Direbobin  Jami'ar mai suna Ali Dauda wanda ya rasu a jamhuriyyar kasar Nijer. 


Ali Dauda ya rasu ne a ranar Juma'a 23 ga watan Yulin 2021 bayan gajeruwar rashin lafiya. 


Sakon ta'aziyyar na dauke da sa hannun Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo inda a ranar Asabar aka rabawa manema labarai a Kano. 

Farfesa Abubakar Gwarzo ya bayyana rasuwar Ali Dauda a matsayin babban rashi ba kawai ga iyalinsa ba har ga dukkanin ma'aikatan Jami'ar. 


Ya bayyana Marigayin a matsayin jajirtacce wanda ya bada gudummawa sosai wajen ci gaban Jami'ar. 


Farfesa Adamu Gwarzo ya yi addu'ar Allah ta'ala ya jikan Marigayin ya kuma sanya shi a madaukakiyar aljannah Firdaus, sannan kuma ya bai wa iyalai hakurin jure rashin da suka yi. 

"a madadin hukumar gudanarwa ta MAAUN, ina mika ta'aziyyata ga iyalai, 'yan'uwa da abokan arziki na mamacin", a sakon ta'aziyyar. 

Ya karkare da cewa; "Allah ta'ala ya jikansa da Rahama, ya gafarta masa ya sanya Aljannah Firdaus ta zama makoma", inji Farfesa Adamu Gwarzo.

Post a Comment

0 Comments