Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami'ar MAAUN Ta Taya Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Murna Bisa Mukamin Shugabancin Majalisar Kasuwanci Ta Faransa-Nijeriya Da Aka Ba shi

Shugaba kuma mu'assasin rukunin jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ...Shugaba kuma mu'assasin rukunin jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya shugaban gamayyar Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabi'u murna bisa mukamin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ba shi na ya jagoranci majalisar kasuwanci ta Faransa da Nijeriya. 

Sakon taya murnar na dauke ne da sa hannun Farfesa Abubakar Gwarzo wanda aka rabawa manema labarai a ranar Alhamis a Kano. 


Shugaban rukunin jami'o'in MAAUN din, ya bayyana mukamin da aka bai wa babban dan kasuwar Abdul Samad na ya jagoranci majalisar kasuwancin ta Faransa da Nijeriya a matsayin 'mukamin da ya dace' idan aka yi duba da gagarumin gudummawar da ya bayar wajen bunkasa bangaren tattalin arziki da ci gaban kasarnan musamman gudummawarsa ta baya-bayan nan a lokacin yaki da annobar cutar korona a kasarnan. 


A cewar Farfesa Gwarzo, nada Abdul Samad Rabi'u a matsayin shugaban majalisar kasuwancin zai taimaka matuka gaya wajen karfafa alakar cinikayya da kasuwanci a tsakanin Nijeriya da Faransa. 

"a madadin kaina da iyalina da hukumar gudanarwa ta jami'ar MAAUN ina taya ka murna bisa wannan mukamin a matsayin shugaban majalisar kasuwanci ta Faransa da Nijeriya", inji shi. 

"Ina addu'ar Allah ta'ala ya taimake ka wajen sauke nauyin da aka dora maka a sabon mukamin nan", cewar Farfesa Abubakar Gwarzo a sakon taya murnar. 


A karshe ya mika sakon godiya ga gwamnatin Faransa a karkashin shugabancin Emmanuel Macron bisa zakulo Abdul Samad Rabi'u ya ba shi wannan mukamin.

No comments