Jami’ar MAAUN Ta Taya Tsohon Dalibinta Murnar Mukamin Shugabancin HRORBN Da Ya SamuHukumar gudanawar ta Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) dake jamhuriyyar kasar Nijer, ta taya tsohon dalibinta Babagana Mustapha murna bisa mukamin shugabancin hukumar tattara rijistar bayanai ta lafiya ta Nijeriya (HRORBN) da aka ba shi . 

Takardar taya murnar na dauke da sa hannun shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo wanda ya aiko daga birnin Paris kuma aka rabawa manema labarai a birnin Tarayya Abuja a ranar Lahadi.  

A cikin sakon taya murnar, shugaban Jami’ar ta MAAUN, ya ce matashin, Babagana Mustapha ya cancanci mukamin da aka ba shi, domin jajirtacce ne wajen aiki. 

Farfesa Gwarzo ya ce; “MAAUN na alfahari da wannan mukamin bisa duba da cewa ya cancanta sakamakon kwarewarsa a fannin abin da ya karanta da kuma dimbin ilimin da yake da shi a bangaren hulda da jama’a da abubuwan da ke faruwa a duniya”. 

“hukumar gudanarwa ta jami’ar tana taya ka murna tare da mika sakon farin ciki bisa wannan mukamin”, inji Farfesa Abubakar Gwarzo. 

Sanarwar har wala yau ta nemi Mustapha da ya zama jakada nagari ga jami’arsa da ya kammala a yayin gudanar da ayyukansa, inda ta nemi da kuma ya sanya tsoron Allah a aikinsa. 

A karshe ya yi addu’ar Allah ya taimake Mustapha ya kuma ba shi basirar sauke nauyin da aka dora masa, sannan ya nemi da ya sanya adalci da daidaito a yayin aikinsa. 


Post a Comment

0 Comments