MADOGARA ta labarto cewa; Babbar kotu a Kaduna ta bada umurnin a saki Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakz...
MADOGARA ta labarto cewa; Babbar kotu a Kaduna ta bada umurnin a saki Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddeen Ibrahim tare da wanke su daga dukkanin zarge-zargen da gwamnatin Kaduna ke musu guda takwas.
Kotun ta bada umurnin ne a zamanta na yau Laraba 28 ga watan Yulin 2021 daidai da 18 ga watan Zulhijjah, 1442 a yayin yanke shari'ar da aka kawashe tsawon shekaru biyu ana yinta.
Mai shari'a Gideon Kurada ne ya yanke hukuncin.
No comments