A yau Litinin 12 ga watan Yulin 2021, Jaridun Nijeriya sun haÉ—a kai wajen wallafa abu iri É—aya a shafukan farko na jaridunsu a matsayi...
A yau
Litinin 12 ga watan Yulin 2021, Jaridun Nijeriya sun haÉ—a kai wajen wallafa abu
iri ɗaya a shafukan farko na jaridunsu a matsayin nuna adawa kan wasu ƙudurin
dokoki biyu da suke kallonsu a matsayin hanyar daƙile ƴancin faɗin albarkacin
baki a ƙasar.
A
shafukan sun wallafa hoton yaro da aka zana ƙarafan kurkuku a fuskarsu tare da
rubuta "ƙin wallafa labarai."
Ƙudurorin
dokokin na Majalisar Sanya Ido kan Jaridu NPC da kuma Hukumar Kula da Kafafen
Yaɗa Labarai ta ƙasar NBC sun sanya tarar naira miliyan biyar ga ƴan jarida da
gidajen yaÉ—a labarai waÉ—anda "ba sa tabbatar da gaskiya da ingancin
ayyukansu."
Idan
ƙuduran suka zama doka, za a ɗaure duk wanda aka kama da laifin tsawon shekara
uku.
A
watan da ya gabata shugaban kwamitin yaÉ—a labarai na majalisar Dattijai Sanata
Ajibola Basiru, ya kare ƙudurin dokokin.
No comments