Kungiyar Shi'a Ta RAAF Ta Nemi Malaman Kano Su Yi Sulhi Da Abduljabbar Kamar Yadda Sayyadi Mu'awiyyah Ya Yi Da Sayyadina Hassan

Kungiyar Shi'a ta Rasulul A'azam a karkashin Jagorancin Shaikh Nura Dass ta yi kira ga gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Majalisar Malamai ta Kano, Mujamma'u Ashabil Kahfi da daukacin al'ummar Kano da kasa baki daya cewar a yi sulhu da Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara kamar yadda Imam Hassan ya yi sulhu da Sayyadina Mu'awiyyah Bin Anu Sufyan. 

RAAF ta bayyana hakan ne a sakon da ta aikewa Jaridar MADOGARA dauke da sa hannun Sakataren kungiyar na kasa, Saleh Muhammad Sani Zariya a ranar Laraba 14 ga watan Yulin 2021. 


RAAF din ta fara da cewa; "mu'assasar Rasulul A'azam tana kira ga bangarorin da abin ya shafa, kai tsaye ko a fakaice wato gwamnatin mai girma Khadimul-Islam, Fadar mai Martaba Sarkin Kano, majalisar Malamai masu daukaka ta Kano, Mujamma'au Ashabil Kahfi mai daukaka, daukacin al'ummar Kano da kasa baki daya, cewa wannan lamari da ya taso tsakanin Malamai yana da kyau mu yi koyi da sulhun Imamu Hassan dan Ali da Sayyidina Mu'awiyyah dan Abu Sufyan; don mu gudu tare mu tsira tare", inji sanarwar. 

Har wala yau sanarwar ta ci gaba da cewa; "kuma mu wanzar da zaman lafiya a garin Kano da kasa baki daya, tare da la'akari da irin kalubalen tsaro da kasar mu, musamman arewacin Nijeriya ke fuskanta", ta jaddada. 

A karshe sun karkare da cewa; "mu tuna da koyarwar Alkur'ani mai girma "sulhu alheri ne", suka lurantar. 

Ana dai ci gaba da dambarwa tsakanin Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Malaman Kano daga bangarorin Darikar Tijjaniyah, Kadiriyyah, Izala, da kuma Salafiyya bisa zargin da suke yi wa Shaikh Abduljabbar na 'batanci ga fiyayyen halitta Manzon Allah (SAWW)', zargin da Shehin Malamin ke tabbatar da cewa sharri ne ake masa, domin shi kokarin kore 'batanci ga Annabi (S)' yake yi ba " tabbatarwa" ba, inji shi. 

A ranar Asabar ne Gwamnatin Kano a karkashin ma'aikatar lura da addini ta shirya taron 'mukabala', inda dukkanin bangarorin suka halarta, sai dai bayan 'mukabalar' da aka kwashe awa biyar ana yi, Alkalin mukabalar ya bayyana cewa Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara bai iya amsa tambaya ko daya da aka yi masa ba, zargin da Shehin Malamin ya yi watsi da shi a wani sabon murya da ya fitar bayan mukabalar. 


               Kwafen Takardar

Post a Comment

0 Comments