Kurt Westergaard: Ɗan Ƙasar Denmark Da Ya Yi Zanen Ɓatancin Manzon Allah (S) Ya MutuMai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen batanci da ya yi kan fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) ya mutu.

Ya mutu yana da shekaru 84 bayan ya sha fama da jinya, kamar yadda iyalansa suka shaida wa jaridar Berlingske a ranar Lahadi.

Westergaard mai zanen barkwanci ne a jaridar nan mai ra'ayin ƴan mazan jiya ta Jyllands-Posten a farkon shekarun 1980.

Ya yi suna ne a shekarar 2005 bayan wani zanen ɓatanci da ya yi ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (S) a jaridar.

Bayanai sun nuna  cewa; an wallafa zanen ne a shekara ta 2006. Kurt Westergaard sai da ya yi zane goma sha biyu na batanci ga Musulunci.

Zanen da ya ɗaga hankalin al'ummar Musulman duniya. Zanen barkwancin ya jawo zanga-zanga a Denmark da sauran ƙasashen Musulmai.

A baya an yi hakon Westergaard don kashe shi, kuma ala tilas ya rasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar 'yan sanda.

A shekarun ƙarshe na rayuwarsa, dole Westergaard ya dinga zama da masu tsaron lafiyarsa a wani ɓoyayyen waje.

Post a Comment

0 Comments