Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwalara Ta Kashe Mutum 325 A Nijeriya

  BBC Hausa ta labarto cewa; Cutar kwalara ta kashe mutum 325 a Najeriya tun daga watan Janairun 2021 zuwa 27 ga watan Yuni, a cewar Dr Chik...

 


BBC Hausa ta labarto cewa; Cutar kwalara ta kashe mutum 325 a Najeriya tun daga watan Janairun 2021 zuwa 27 ga watan Yuni, a cewar Dr Chikwe Ihekweazu shugaban hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta NCDC.

Dr Ihekweazu ya faɗa wa kamfanin labarai na NAN ranar Asabar cewa an samu mutum 1,786 da suka kamu da cutar a jiha shida daga 20 zuwa 26 ga watan Yuni.

Jihohin su ne: Bauchi (1,239), Kano (362), Neja (62), Zamfara (55), Kaduna (59), Filato (9).

A cewarsa, daga 13 zuwa 19 ga Yuni, jiha biyar - Bauchi, Kano, Kaduna, Filato, Zamfara - sun samu mutum 1,757 da ake zargin sun kamu da cutar.

Jihohin da cutar ta ɓulla zuwa yanzu su ne: Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, Kano, Kaduna, Filato, Kebbi, Cross-River, Nasarawa, Neja, da kuma Abuja.


No comments