Tawagar kwallon kafar Ivory Coast ta buga canjaras da mai rike da kofin wasan kwallon kafa a gasar Olympic, Brazil a ranar Lahadi, inda su...
Tawagar kwallon kafar Ivory Coast ta
buga canjaras da mai rike da kofin wasan kwallon kafa a gasar Olympic, Brazil a
ranar Lahadi, inda suka tashi wasa babu ci, a wasan kwallon kafa na maza da ke
gudana a gasar wasannin motsa jiki ta Olympic a birinin Tokyo na Japan.
Tawagar Brazil, wadda lashe gasar
kwallon kafa ta Olympic a karon farko
cikin shekaru 5 da suka wuce a gida, a lokacin da aka yi gasar a birnin Rio na
daf dora kanta a turba ta zuwa matakin sili daya kwale a Yokohama, amma Ivory
Coast ta hana ta.
An ma yi sa’a lamarin ya takaita a
haka, saboda ta shafe tsawon sa’a guda tana wasan da mutane 10 saboda a minti
na 13th aka baiwa dan wasan tsakiyar Brazil mai wasa a Aston Villa Douglas Luiz
jan kati sakamakon rafke Youssouf Dao da yayi a yayin da yake daf da saka
kwallo a raga.
Sai dai a kusan karshen wasan an bai
wa Eboue Kouassi na Ivory Coast jan kati, lamarin da ya daidaita al’amura a
tsakanin bangarorin.
Brazil ke jan ranagamar rukunin D da
yawan kwallaye, gabanin wasanta da Saudiyya.
No comments