Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwamitin Yaƙi Da Korona Ya Shawarci Masarautar Kano Ta Soke Hawan Sallah

  BBC Hausa ta labarto cewa; Kwamatin yaƙi da cutar korona na Gwamnatin Tarayyar Najeriya ya saka jiha shida da kuma Abuja cikin mafiya haɗa...

 


BBC Hausa ta labarto cewa; Kwamatin yaƙi da cutar korona na Gwamnatin Tarayyar Najeriya ya saka jiha shida da kuma Abuja cikin mafiya haɗarin yaɗuwar cutar sannan ya shawarce su da su soke bukukuwan Babbar Sallah.


Shugaban kwamatin Presidential Steering Committee (PSC) kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Asabar.


Ya zayyana jihohin kamar haka: Legas, Kano, Kaduna, Oyo, Rivers, Filato da Abuja. Mista Mustapha ya ce shi kansa fitar da jerin sunayen mataki ne na yaƙi da yaɗuwar cutar.


"Waɗannan matakan na da muhimmanci sosai yayin da muke ganin ƙaruwar masu kamuwa da cutar a Najeriya," a cewarsa.


"Kwamatin PSC na taya Musulmai murnar Eid-el-Kabir (Idin Babbar Sallah). Sai dai yana shawartar gwamnatocin jiha da shugabannin addini da su san cewa akwai yiwuwar yaɗuwar cutar duk sanda aka tara dubban jama'a."


Saboda haka ne kwamatin ya shawarci jihohin da su soke Hawan Sallah sannan kuma a yi Sallar Idi a masallatan Juma'a.


Matakin ya biyo bayan ɓullar nau'in cutar mai suna Delta a jihohin ƙasar da kuma ƙaruwar masu kamuwa da ita da waɗanda ake kwantarwa a asibiti.

No comments