Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwanaki 40 Da Sace Daliban Makarantar Islamiyyah A Jihar Neja

  Binciken Jaridar LEADERSHIP ya gano cewa, mafi yawan daliban da aka sace na  makarantar Tanko Salihu Islamiyya, Tegina, jihar Neja,  ba s...

 


Binciken Jaridar LEADERSHIP ya gano cewa, mafi yawan daliban da aka sace na makarantar Tanko Salihu Islamiyya, Tegina, jihar Neja, ba su da lafiya kuma da kyar suke tafiya.

Yanayin da daliban 136 suke ciki, wadanda suka kwashe kwanaki 40 a tsare, ya zama babban abin damuwa ga wadanda suka sace su, masu garkuwan suna canza wa yaran ma buya duk bayan kwana uku don gudun kar agano su.

Sakamakon haka, an ce masu garkuwan sun rage kudin fansa daga miliyan N110 zuwa miliyan N50. Da da farko miliyan N200 suka nema na kudin fansa.

Wasu daga cikin iyayen yaran, wadanda suka nemi a sakaya sunan su, sun ce sun samu labari daga masu garkuwan cewa, wasu daga cikin yaran da kyar suke iya cin abinci ko tafiya, kuma babu wani likita da zai duba lafiyarsu, Panadol ko Paracetamol ne kawai akwai don rage zafin ciwon dake damun yaran.”

No comments