Mahajjatan
bana sun yi amfani da tsakuwar da aka
feshe ta da maganin kashe kwayar cuta wajen jifan shaidan a wannan Talatar tare
da mutunta ka’idojin yaki da annobar Korona kamar yadda Rfi Hausa suka labarto.
Da
safiyar jiya ne, wani karamin adadi na mahajjatan ya doshi Jamratul Aqabah na
Mina da ke kusa da birnin Makka domin jifan shaidan.
Mahajjatan
sanye da takunkumi da kuma hirami, kowannensu ya yi amfani da tsakuwa
bakwai-bakwai wajen jifan shaidan, tsakuwar da aka killace ta a cikin kananan
jakunkuna.
A
wasu shekarun baya, an samu asarar dubban rayukan mahajjata a wurin jifan
shaidan a sanadiyar turmutsitsi da aka samu, amma a bana ba a samu irin wannan
matsalar ba, inda ma Alhazan suka samu damar walawa sosai tare da ba su
kwarya-kwaryar kariya.
Shekaru
biyu kenan a jere da mahukuntan Saudiya suka takaita adadin mahajjata zuwa dubu
60 da zummar dakile yaduwar cutar Korona.
Aikin
hajji dai, daya ne daga cikin shika-shikan Musuluci biyar wanda ke zama wajibi
ga Musulmin da ya samu iko kuma sau daya tal a rayuwarsa.
0 Comments