Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar kora tare da kame Dakataccen shugaban Hukumar karbar korafe-korfen da hana da cin hanci da ...
Majalisar
Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar kora tare da kame Dakataccen shugaban
Hukumar karbar korafe-korfen da hana da cin hanci da rashawa na jihar Kano,
Muhuyi Magaji Rimin Gado ba tare da bata lokaci ba.
An
gabatar da wannan kudurin ne a lokacin zaman majalisar wanda Injiniya Hamisu
Ibrahim Chidari ya jagoranta.
Yayin
gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wucin gadi Wanda Majalisar ta kafa Alhaji
Umar Musa Gama ya bayyana cewa kwamitin Mai mambobi 12 sun kammala bincike kuma
sun tsara shawarwari 5 da za a gabatar.
Ya
yi nuni da cewa shawarwarin sun hada da korar shugaban da aka dakatar nan take,
kamawa da gurfanar da Muhyi tare da kafa wani kwamiti na wucin gadi da zai
binciki ayyukan kudi na Hukumar karbar korafe-korfe da yaki da cin hanci da rashawa
daga shekarar 2015 zuwa yau.
Da
yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman, shugaban masu rinjaye na
majalisar, Alhaji Labaran Abdul Madari ya ce kwamitin hadin gwiwar da majalisar
ta kafa don binciken Muhyi ya gano cewa rahoton likitan da lauyan shugaban da
aka dakatar ya gabatar karya ne.
Ya
lura cewa kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa Shugabar ma’aikatan gwamnati ta
jiha ta dauki matakin da ya dace a kan Isah Yusif wani jami’i Mai Matakin
albashi na hudu da ke aiki a matsayin akawu a hukumar karbar korafe-korfen
jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.
Alhaji
Labaran ya ce kwamitin ya kuma yi kira ga akawun da Muhyi ya ki amincewa da shi
daya fara aiki da wuri-wuri a Hukumar.
Idan
za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa majalisar dokokin jihar Kano ta karbi
korafi daga ofishin babban akawun jiha game da kin amincewa da wani babban
akawun da aka dakatar da shi da shugaban da aka dakatar ya tura.
No comments