Daga Muhammad A. Dalhatu MADOGARA ta labarto cewa; wani masani ya bayar da shawarar cin naman zomo ga masu shekaru 40 zuwa sama domin...
Daga Muhammad A. Dalhatu
MADOGARA ta labarto cewa; wani masani ya bayar da
shawarar cin naman zomo ga masu shekaru 40 zuwa sama domin kariya daga kamuwa
daga cutar ‘uric Acid’.
Dr Huzaifa Abdullahi, Likitan dabbobi a Asibitin
Dabbobi na jihar Bauchi, shi ne ya bayar
da wannan shawarar a yayin hirar da ya
yi da Kamfanin Dillancin Labaran
Nijeriya, NAN, a ranar Lahadi A Bauchi.
Dr Abdullahi ya tabbatar da cewa naman zomo na da
sinadarai masu karfi na gina jiki, kuma naman na dauke da kitse mai kauri.
“mafi yawan mutane ba su san yadda naman zomo yake
da sinadaran gina jiki ba. Dabbar na da karancin cutarwa kuma tana hana mutum
kamuwa da cutar ‘uric acid’”, inji shi.
A cewarsa sabanin shanu da sauran dabbobin gida,
naman zomo yana daya daga cikin dabbar
dake da farin tsoka.
A cewar masanin idan al’umma suka yi amfani da
shawarwarin masana wajen cin naman zomo hakan zai hana al’umma kamuwa daga
cututtukan da dan Adam ke harbuwa da shi daga dabbobi.
Ya kara da cewa; “mutanen dake da shekaru daga 40
zuwa sama ana yawan samun su da cutar ‘uric acid’, kuma jan nama yana taimakawa
wajen haifar da cutukan nan ga al’umma”, ya tabbatar.
A cewar Dr Abdullahi, cutar ‘uric acid’ na haifar
da ciwon kafa kuma yana da hatsarin gaske ga rayuwar mutane.
No comments