Masarautar Kano Ta Bi Umurni Ta Soke Hawan Sallah

 Daga Muhammad A. Dalhatu

Rahotannin dake shigo mana na nuni da cewa; masarautar Kano ta soke bukukuwan hawan Babban Salla.

Kafar watsa labarai  ta Solacebase ta labarto cewa; masarautar ta soke bukukuwan sallar ne sakamakon shawarwarin da gwamnatin Tarayya ta bayar saboda dawowar annobar cutar korona a karo na uku.

Madakin Kano, Alhaji Yusuf  Nabahani ya tabbatar da ‘yan jarida hakan  a yau Litinin.

Alhaji Yusuf Nabahani ya ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ba shi umurnin ya sanar da dukkanin Hakiman dake karkashin masarautar wannan umurnin.

Dama MADOGARA  ta labarto cewa; kwamitin dake yaki da annobar cutar korona ta gwamnatin Tarayya a karkashin ofishin  Sakataren gwamnatin  Tarayya ta shawarci jihohi shida ciki harda birnin Tarayya Abuja da su soke bukukuwan Sallah domin cutar korona ‘yar Delta ta dawo gadan-gadan  a kasar.

Jihohin sun hada da Legos, Oyo, Ribas, Kaduna, Kano, da Filato.

 


Post a Comment

0 Comments