Masarautar Daura da ke Jihar Katsina ta dakatar da Hawan Sallah a bikin Babbar Sallah da za a yi sakamakon "rashin tabbataccen tsaro&...
Masarautar Daura da ke Jihar Katsina ta dakatar da
Hawan Sallah a bikin Babbar Sallah da za a yi sakamakon "rashin tabbataccen
tsaro".
Wata sanarwa da Danejin Daura Abdulmumini Salihu ya
fitar ranar Talata ta ce Sarki Umar Faruq Umar ya É—auki matakin ne sakamakon
matsalolin tsaro da suka addabi yankin masarautar.
"A maimakon haka, za a gudanar da Sallar Idi
kamar yadda aka saba, bayan an kammala za a gudanar da addu'o'i na musamman a
fadar mai martaba sarki don neman dawwamammen zaman lafiya," in ji
sanarwar.
Al'ummar Musulmi a Najeriya za su gudanar da bikin
Babbar Sallah ranar 10 ga watan Zul Hijja na shekarar Hijira ta 1442, wanda ya
yi daidai da 20 ga watan Yuli.
Garin Daura wanda shi ne mahaifar Shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari, na fama da hare-haren 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi
ne waÉ—anda ke sace mutane da kashe su don neman kuÉ—in fansa.
No comments