Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Murar Tsuntsaye Ta SanyaGwamnatin Ghana Kashe Kaji 4,500

  Gwamnatin Ghana ta kashe kaji dubu hudu da dari biyar tare da hana zriga-zirga da su bayan an samu kusan 6,000 da suka mutu sakamakon mura...

 


Gwamnatin Ghana ta kashe kaji dubu hudu da dari biyar tare da hana zriga-zirga da su bayan an samu kusan 6,000 da suka mutu sakamakon murar tsuntsaye mai suna H5N1.

Shugaban ma'aikatar dabbobi ta ƙasar ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa kajin sun fito ne daga gona bakwai da ke Tsakiyar Birnin Accra da kuma Yankunan Volta.

Patrick Abakeh ya ƙara da cewa yanzu haka an dakatar da zirga-zrigar kaji a yankunan.

Kazalika, Ghana ta dakatar da shigar da kaji ƙasar daga ƙasashen Nijar da Nijeriya da Togo da Burkina Faso da Mauritania da Senegal a matsayin matakin ko-ta-kwana.

Wannan ne karo na huɗu da annobar murar tsuntsayen take ɓarkewa a Ghana tun 2015.


No comments