Mutum 150 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Sun Shaƙi Isakar Ƴanci


 

Aƙalla mutum 150 daga wasu ƙauyuka a Ƙaramar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara ne ƙasurgumin shugaban ƴan bindigar nan da ake ƙira Turji ya sako a yau Lahadi.

Aminiya ta ruwaito Turji ya sako mutanen da ya yi garkuwa da su ne bayan jami’an tsaro sun saki mahaifinsa da ke tsare a hannunsu.

A wani naɗaɗɗen audio da ke yawo a kafafen sada zumunta, anji Turji yana cewa jamu’an tsaro sun kama mahaifinsa a jihar Jigawa ba tare ya yi msu komai ba.

Tun bayan kama mahaifin ne ɗan ta’addan ya sha alwashin ƙaddamar da hare-hare a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara inda ya yi ta sa yaransa syna kama masa mazauna ƙauyukan yana garkuwa da su.

Post a Comment

0 Comments