Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Za Ta Binciki Zargin Rashawa Kan Abba Kyari

Bbc Hausa ta labarto cewa; Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce ta ba da umarnin yin abin da ta kira nazari kan zargin karɓar...


Bbc Hausa ta labarto cewa; Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce ta ba da umarnin yin abin da ta kira nazari kan zargin karɓar cin hanci da aka yi wa ɗaya daga cikin jami'anta DCP Abba Kyari.

Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sandan Nijeriya, Frank Mba ya fitar ta ce rundunar 'yan sandan ƙasar na jaddada ƙudurinta wajen tabbatar da adalci da ƙarfafa dangantakar aiki da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI da kuma sauran aboka ƙawance.

Wannan lamari na zuwa ne bayan wata taƙaddama ta ɓullo tsakanin matashin ɗan Najeriyan nan da ke fuskantar tuhuma a Amurka kan alaƙa da manya-manyan ayyukan zambar kuɗi na duniya, Raymond Abbas, da aka fi sani da Hushpuppy da kuma fitaccen ɗan sandan ƙasar Abba Kyari.

Wasu bayanai da matashin ya fada wa masu bincike na cewa ya taɓa bai wa Abba Kyari wasu kuɗaɗe domin a ɗaure wani abokin hulɗarsa, zargin da ɗan sandan ya musanta.

Jaridun Nijeriya da dama dai sun yayata wani rahoto a yau cewa kotun Amurka ta ba da umarnin kamo Abba Kyari. 

No comments