Shin Da Gaske ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 15 A Asibitin Kutare A Zariya?

 


Rahotanni  sun bayyana cewa wadansu ƴan bindiga sun afka gidajen ma’aikatan asibitin Kutare a garin Zaria suka yi awon gaba da mutum 15.

Wani ma’aikacin asibitin ya shaida wa BBC cewa mutanen da ƴan bindigar suka sace sun ƙunshi maza da mata da kuma ƙananan yara.

Ya ce an ƴan bindigar sun kai harin ne tsakiyar dare zuwa wayewar safiyar Lahadi.

Wasu rahotanni sun ce cikin mutanen da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su har da jarirai.

Zuwa yanzu gwamnatin Kaduna da rundunar ƴan sandan jihar ba su fitar da sanarwa ba game da harin.


Post a Comment

0 Comments