Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Halaka Mayakan Boko Haram 13 A Nijar

  Hadin gwuiwar rundunar sojojin kasashen Afirka ta Yamma ta yi nasarar kashe mayakan Boko haram 13 a fafatawar da suka yi da su a kudu maso...

 


Hadin gwuiwar rundunar sojojin kasashen Afirka ta Yamma ta yi nasarar kashe mayakan Boko haram 13 a fafatawar da suka yi da su a kudu maso gabashin kasar, abin da ya kai ga kashe fararen hula guda 4.

Sanarwar da dakarun suka gabatar ta ce mayakan a cikin motoci goma sun yiwa sojojin kwantar bauna ne  yammacin talata akan hanyar Diffa zuwa Maine Soro amma sai yunkurin na su ya kasa cimma biyan bukata inda sojojin suka bude musu wuta.

Rahotanni sun ce kafin harin, mayakan sun tare wata motar safa daga bisani kuma suka kai hari akan wasu mazauna kauye inda suka kashe mutane 4, cikin su harda direban motar da Sarkin kauyen.

Sanarwar sojin tace dakarun su guda 4 sun samu raunuka a fafatawar da suka yi, yayin da su kuma suka kashe mahara 13 daga cikin su da kuma kwashe makamai da motar su guda.

Mayakan boko haram dake dauke da makamai sun zafafa kai hare hare a Diffa dake Jamhuriyar Nijar kusa da Yankin Tafkin Chadi tun daga watan Mayu.

Ko a watan jiya mutane kusan 6,000 da suka tsere daga garuruwan su sakamakon karuwar hare hare a Yankin sun fara komawa garuruwan su.

Akalla mutane 300,000 da suka fito daga Najeriya da Nijar ke zaman gudun hijira a Yankin Diffa abin da ya sa shugaban kasa Bazoum Mohammed ya kaddamar da shirin mayar da su garuruwan su.


No comments