Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojojin Najeriya Sun Dakile Wani Hari Da Mayakan IPOB Suka Kai Masu A Inugu

  Sojojin Nijeriya da aka tura don hana ayyukan 'yan bindiga a unguwar Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Inugu sun dakile wani ...

 Sojojin Nijeriya da aka tura don hana ayyukan 'yan bindiga a unguwar Adani a karamar hukumar Uzo-Uwani ta jihar Inugu sun dakile wani hari da mayakan kungiyar aware ta IPOB suka kai da bindigogi kan shingen sojijin a ranar Talata.

Wata sanarwa da Birgediya Janar Oyema Nwachukwu, Kakakin rundunar sojin Nijeriyar ya fitar ta ce an kashe sojoji biyu a yayin musayar wuta da 'yan bindigar.

Haka zalika, ya bayyana cewa ana ci gaba da kokarin kamo maharan da suka kai harin.  Sannan ya bukaci al'ummar yankin su taimaka wa jami'an tsaro wajen zama masu bin doka da samar da bayanai kan duk wani bata-gari domin dakile ayyukansu.

No comments