Wasu ‘yan Nijeriya sun bukaci baiwa rundunonin sojin kasar goyan bayan da suke bukata saboda yaki da Yan ta’adda da masu aikata laifuffuka...
Wasu
‘yan Nijeriya sun bukaci baiwa rundunonin sojin kasar goyan bayan da suke
bukata saboda yaki da Yan ta’adda da masu aikata laifuffuka da suke yi a sassan
Najeriya wanda yayi sanadiyar hallaka sojojin 183 daga cikin su a cikin watanni
6 da suka gabata.
Wani
binciken da Jaridar Daily Trust tayi yace tsakanin watan Janairu zuwa Yunin
bana yace sojoji 183 suka mutu kuma akasarin su sun rasu ne a bakin daga lokacin
da suke kokarin yaki da masu aikata laifuffuka domin kare lafiyar jama’ar kasa.
Rahotanni
sun ce dubban sojojin Nijeriya yanzu haka da suka hada da sojin kasa da na sama
da na ruwa ke aikin samar da zaman lafiya a jihohin kasar sama da 30 saboda tabarbarewar
tsaron da ya addabi kasar.
Binciken
jaridar yace akasarin sojojin da suka mutu sun rasa rayukan su sakamakon harin ‘yan
bindiga da zauna gari banza da mayakan boko haram da ‘yayan kungiyar asiri da
na ‘yan fashi.
Rahotan
yace an kashe sojojin ne a sassa daban daban na Najeriya amma akasarin su sun
mutu ne a yankin arewa maso gabas da ake yaki da kungiyar boko haram.
Binciken
yace daga cikin sojoji 183 da aka kashe, kungiyar boko haram da ISWAP sun kashe
114 daga cikin su, yayin da 69 kuma suka mutu a wasu hare hare daban daban.
Jaridar
ta bayyana jihohin da aka kashe sojojin da suak hada da Borno da Yobe da Jigawa
da Kaduna da Niger da Nasarawa da Benue da Ebonyi da Enugu da Delta da Cross
River da Rivers da kuma Bayelsa.
A
ranar alhamis da ta gabata, Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu ya sanar da cewar
sojoji 7 suka mutu a jihar sa lokacin da suke fafatawa da yan bindiga a kauyen
Marke, yayin da wasu 5 suka samu raunuka.
Jaridar
ta ce a Yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu ‘Yayan haramcaciyar kungiyar
IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra da reshen ta dake dauke da makamai na ESN
sun kashe sojoji da dama a hare haren da suke kaiwa a yankin.
Ko a
wannan makon sanda sabon shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Faruk
Yahaya ya ziyarci asibitin soji dake Kaduna domin duba sojojin da suka samu
raunuka a filin daga.
Wani
masanin harkar tsaro Kabiru Adamu ya shaidawa jaridar cewar rashin isassun
kayan aiki na zamani da suka hada da rigar sulke da samun bayanan asiri na daga
cikin abinda ke haifar da kisan sojojin.
Adamu
ya ce wasu kayan aikin da dakarun Nijeriya ke amfani da su a yakin da suke da
kungiyar boko haram basu da ingancin da ake bukata.
Wani
jami’in Majalisar Dinkin Duniya Chukwuma Ume yace yaki a wannan zamani ya wuce
amfani da bindiga kirar AK 47 saboda ci gaban zamani da aka samu.
Ume
yace sojojin Najeriya na bukatar makamai na zamani da bayanan asiri wajen
murkushe duk wadanda suka dauki makamai suna aikata laifuffuka.
No comments