Kungiyar Daliban Nijeriya ta kasa da aka fi sani da NANS ta yi watsi da wani kudirin da ke gaban majalisar dokokin Nijeriya a yanzu haka w...
Kungiyar Daliban Nijeriya ta kasa da
aka fi sani da NANS ta yi watsi da wani kudirin da ke gaban majalisar dokokin Nijeriya
a yanzu haka wacce ake so a maida shi doka, wanda idan hakan ya tabbata zai
haramta gudanar da duk wata zanga-zanga a kasar.
Shugaban kungiyar, Asefon Sunday, ne
ya yi watsi da wannan kudurin na gaban majalisar a cikin wata sanarwa da ya
gabatar a yammacin jiya Juma'a, inda ya ce dokar karan tsaye ce ga dimokuradiyya
da kuma babban 'yanci na' yan kasa dake da damar gudanar da zanga-zanga.
Shugaban NANS ya ce: za su bi hanyar
da shugabannin kasar ke fahimta wato gudanar da zanga-zanga wajen kawo cikas ga
kudirin dokar dake gaban majalisar.
Ya
ce kudurin, wanda dan majalisa Chinedu Martins na jam'iyyar PDP daga jihar Imo
ya gabatar, NANS ta ce abin takaici ne ganin yadda wakilan al’umma ke kokari
wajen ganin sun haramta musu abin da ke zama hakkin al’ummar.
No comments