Sufeto Janar Na 'Yan Sandan Nijeriya Ya Sha Kaye A Babbar Kotu A Zamfara
Daga Hussaini Kauran Wali

A yanzu haka Babbar kotu ta hudu dake jihar Zamfara, ta wanke tuhuma shida da ake yi wa Babban Dan kasuwar nan Alhaji Muhammad Garba Tugana da Shugaban 'Yan sanda na Kasa ya gurfanar a Zamfara.

Mai shari'a Bello Muhammad Tukur Gumi, ya wanke Dan kasuwan bayan tsawon shekaru uku ana yin shari'ar a Babbar Kotu ta hudu dake Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Sufeto Janar na 'yan sanda na kasarnan ya kai Babban dan kasuwa mai sana'ar Walda Muhammad GarbaTugana tare da yaransa su biyu Bala Yunusa da Hussaini Abba akan zargin su da mayyan laifuka a Babbar kotu ta hudu dake Gusau a shekara 2018.

Bayan jin ta bakin wadanda aka kai kara da kuma wanda ake tuhuma da shedun kowanne sashe tare da lauyoyinsu, a karshe mai shari'a Bello Muhammad Tukur Gumi, ya tabbatar da cewa, Muhammad Garba Tugana da mutane biyu da Sufeto Janar na 'yan sanda ke kara a kotu bata kama su da wani laifi ba, a don haka ta sallame su.

Manema labarai sun nemi jin ta bakin lauyan Sufeto Janar na 'yan sanda bayan yanke hukuncin Shari'ar, Barista I.A Bawa akan hukuncin kotu ya bayyana cewa, shi bai taba zuwa wannan shari'a ba sai a yau domin lauya Jafaru ne ke bin shari'ar; "a don haka babu abin da zance", inji Lauyan Sufeto Janar.

Shi kuwa lauyan wanda ake kara, Barista A.A.Jibirila ya bayyana godiyarsa ga Allah da gaskiya ta bayyana akan zaluncin da ya ce an yi wa wanda yake karewa. Kuma Mai Shari'a Bello Muhammad Tukur Gumi, ya yi adalci akan wannan shari'a domin ya nuna cewa, kotu na ba wanda aka fi karfinsa hakinsa, inji A.A.Jabiril.

Lauyan ya kuma tabbatar da cewa, za su bi hakkin wadannan bayin Allah da aka ci zarafinsu har tsawon shekaru uku.

A nashi jawabin, Babban dan kasuwar Muhammad Garba Tugana ya miqa godiyarsa ga Allah da ya wanke su akan tuhumar kazafi da Sufeto Janar ya yi masa. "Kuma za mu tattauna da Lauyanmu domin neman hakin da cin zarafin da aka yi mana. Ina godiya ga ku 'yan Jaridu da ku kai ta bin shari'ar har ta kai ga shi mun samu nasara", inji shi. 

Post a Comment

0 Comments