Hukumar gudanarwar Jami’ar Legas da ke Nijeriya ta bukaci daliban ta da ke zama a dakunan makarantar da su fice sakamakon samun wasu dalib...
Hukumar gudanarwar Jami’ar Legas da ke Nijeriya ta bukaci daliban
ta da ke zama a dakunan makarantar da su fice sakamakon samun wasu dalibai da
ke dauke da cutar korona.
Mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ya sanar da
matakin bayan wani taron gaggawa da ya jagoran ta yau domin nazarin da ake
ciki.
Oluwatoyin ya ce taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ya yanke
hukuncin dakatar da karatu har zuwa ranar 26 ga wannan watan da za a ci gaba da
kafofin bidiyo.
Tuni asibitin Jami’ar ya sanar da fuskantar abinda ake kira zagaye
na 3 na annobar koronar, kwana guda bayan gwamnatin Lagos ta yi gargadi akai.
A karshen makon da ya gabata Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu ya
sanar da jama’ar Jihar cewar ana fuskantar dawowar annobar karo na 3 sakamakon
karuwar masu harbuwa da ita da aka gani wanda ya tashi daga sama da kashi 1
zuwa sama da kashi 6 da rabi a ranar 8 ga wannan watan.
Ita ma Jami’ar Lagos ta fuskanci karuwar masu zuwa da alamun cutar,
abinda ya sa aka sanar da hukumomin ta domin daukar mataki.
Sashen kula da lafiya na Jami’ar ya ce ya na daukar matakan da suka
dace domin kare lafiyar dalibai da ma’aikatan dake cikin jami’ar.
No comments