Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tunisiya Ta Garkame Dan Majalisa Saboda Sukar Shugaban Kasarsa

  Jami'an tsaron Tunisiya sun kama wani dan majalisar kasar da ya yi kaurin suna wurin sukar shugaban kasar. Dan majalisar Yassin Ayari,...

 


Jami'an tsaron Tunisiya sun kama wani dan majalisar kasar da ya yi kaurin suna wurin sukar shugaban kasar. Dan majalisar Yassin Ayari, ya siffanta rushe gwamnatin da shugaban na Tunisiya ya yi a matsayin juyin mulki.

A ranar Lahadin da ta gabata ce dai shugaban na Tunisiya ya kori firaminista sannan ya dakatar da ayyukan majalisar kasar na wata guda, ya kuma bai wa kansa cikakken iko.

Matar dan majalisar da aka kama din ta ce kusan mutane 20 ne suka kutsa kai cikin gidansu inda suka gabatar da kansu a matsayin jami'an tsaro daga fadar shugaban kasa. Matar ta kuma yi zargin cewa sun yi amfani da karfin tuwo a kan mijin nata kafin su yi awon gaba da dan majalisar mai sukar shugaban kasa.

A gefe guda kuma a wannan Juma'a wata kotu a Tunisiyan ta fara sauraron shari'ar wasu mutane hudu 'yan jam'iyya Ennahda ta Musulmi masu adawa da shugaban kasar, ana kuma zargin su da tayar da hankula bayan rusa gwamnatin da Shugaba Saied ya yi.

No comments