Kungiya
mai zaman kanta ta Babban Gona dake Nijeriya, ta samu rancen dala miliyan 5
daga Majalisar Dinkin Duniya don taimaka wa kananan manoma, matakin da ake sa
ran zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen matsalar karancin abinci da
rashin ayyukan yi.
Shugaban
Asusun Majalisar Dinkin Duniya kan ci gaban Noma (IFAD) Gilbert F. Houngbo ne
ya jagoranci kaddamar da sabon shirin samar da kudaden tallafin da zummar
fadada kokarin magance matsalar yunwa da talauci a kasashe matalauta, ta hanyar
inganta matakan samar da abinci.
Bangaren
asusun majalisar dinkiin duniyar na IFAD mai suna PSFP dake tallafawa kanana da
matsakaitan masana’antu ya sanar da bada tallafin bashin farko na dalar Amurka
miliyan 5 ga Babban Gona kungiya mai zaman kanta dake Najeriya, sakamakon
kokarin da ta yi wajen tallafawa daruruwan kananan manoma wajen fadada ayyukan
noman da suke yi zuwa kaiwa matakin na kasuwanci.
An
dai kiyasta cewar tallafin bashin na dala miliyan 5, zai baiwa kungiyar ta
Babban Gona damar tallafawa kananan manoman Shinkafa da Masara dubu 377 a
Najeriya ta fuskokin samar da kayan aiki, bayar da horo da kuma sayan amfanin
gonar da manoman suka samar, shirin da ake sa ran zai samar da guraben ayyukan
yi akalla dubu 65 da mata zalla, da kuma wasu karin guraben ayyukan yin kimanin
dubu 66 ga matasa nan da shekarar 2025.
0 Comments