Yadda Aka Cafke Sunday Igboho Mai Fafutukar Wargaza Nijeriya

 


Jami’an tsaron Nijeriya sun kama Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa zalla a kasar bayan ya shiga jirgin sama a birnin Kwatano da ke Benin domin tafiya Jamus.

Wani babban jami’in ‘yan sandan Benin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, yanzu haka ana shirye-shiryen tasa keyar Igboho zuwa Nijeriya da zarar kasashen biyu sun cimma matsaya kan wasu sharudda.

Tun a farkon wannan wata na Yuli, jami’an tsaron farin kaya na DSS suka yi yunkurin cafke Igboho a gidansa na garin Ibadan a yankin kudancin Nijeriya.

Sai dai Igboho ya yi nasarar tserewa a wancan lokaci bayan mukarrabansa da ke ba shi kariya sun shafe tsawon sa’a guda suka musayar wuta da jami’an tsaron.
Jami’an tsaron sun gano wasu kayayyaki a gidan Igboho da suka hada da tarin makamai kamar bindigogi da alburusai, sannan suka kama mutane 12 da kuma wata mace guda.

Wannan na zuwa ne bayan hukumomin Nijeriya sun kama Nnamdi Kanu, wanda shi ma ke gwagwarmayar kafa kasar Biayafa mai zaman kanta a yankin kudu maso gabashin kasar.


Post a Comment

0 Comments