Shugaban
Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Kaduna, Joseph Hayab ya bayyana
cewa, an sako daliban Makarantar Bethel Baptist, Demish, Kaduna da aka sace,
bayan tsawon kwanaki 20 da suka shafe a wurin masu garkuwa da mutane.
Jaridar
yanar gizo, TheCable ta ruwaito Hayab na bayyana haka a ranar Lahadi.
Kimanin
Dalibai 121 ‘yan bindiga suka sace a dakunan Kwanan Dalibai na Makarantar a
ranar 5 ga watan Yuli.
“Hayab
bai tabbatar da adadin daliban da aka sako” inji Jaridar TheCable.
Kungiyar
Baptist ta Nijeriya tuni ta gana da wasu Majami’un ta domin tattara kudaden da ‘yan
bindiga suka bukata, domin sako daliban da aka sace a Makarantar Bethel Baptist
High School a jihar Kaduna.
Idan
dai ba a manta ba Jaridar Dimokradiyya ta baku rahoton cewa, a ranar 5 ga watan
Juli Shekarar 2021, da Misalin karfe 2 na dare, Yan bindiga suka shiga
Makarantar dake Karamar Hukumar Chikun tare da tafiya da wasu yara.
Jigon
Makarantar wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Baptist ta Kaduna Reverand
Ishaya Jangado ya ce kimanin dalibai 121 ‘yan bindiga suka sace, inda daga baya
suka saki dalibi daya sakamakon rashin lafiya.
Bayan
an tattauna, ‘yan bindigar wanda suka bukaci miliyan 100 da farko suka rage
kudin ya zuwa naira miliyan 60.
0 Comments