Daga Muhammad Badamasi Wata dalibar Kwalejin ilimi ta gwamnatin Tarayya dake Zariya, wato FCE Zariya ta bace bat a yau Asabar 10 ga wa...
Daga
Muhammad Badamasi
Wata
dalibar Kwalejin ilimi ta gwamnatin Tarayya dake Zariya, wato FCE Zariya ta
bace bat a yau Asabar 10 ga watan Yulin 2021 bayan da ta fita daga gidansu dake
Kaura cikin birnin Zariya zuwa makarantar FCE dake Unguwar Gyallesu duk a
karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.
Lamarin
ya auku ne da safiyar yau Asabar, inda da misalin karfe 9 da mintoci na safe ta
aikawa mahaifiyarta sako cewa; “Mama ina neman addu’arku, na fada hannunsu”.
![]() |
Sakon da ta aikawa mahaifiyarta. |
Mahaifinta
ya shaidawa wakilin MADOGARA cewa; “bayan ta aikawa mahaifiyarta sakon nan, an
kira lambarta ba ya zuwa har ya zuwa yanzu”, kamar yadda ya tabbatar mana.
Dalibar
mai suna Rahmatu A. Sambo tana karatun ‘part-time’ ne a bangaren lissafi da
ilimin sinadarai (Maths/Chemistry).
Wadansu
bayanai sun nuna cewa dalibar ta saba hawa babur ne a duk lokacin da za ta tafi
makaranta daga gida.
Ya zuwa
hada rahoton nan babu cikakken bayanin kan inda dalibar take, sai dai al’umma
na ta tururuwa zuwa gidan iyayen dalibar domin taya su alhini da addu’ar Allah
ya bayyanata.
No comments