Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yan Bindiga A Kaduna Sun Sake Garkuwa Da Basarake

  An sace basaraken masarautar Jaba, a Jihar Kaduna 'Kpop Ham' Johanathan Danladi Gyet Maude kamar yadda rahotanni suka tabbatar. Ba...

 


An sace basaraken masarautar Jaba, a Jihar Kaduna 'Kpop Ham' Johanathan Danladi Gyet Maude kamar yadda rahotanni suka tabbatar. Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigar sun sace Basaraken ne a jihar Nasarawa.

Kakakin ƴan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma shaida cewa an sace Maude a yankin Panda da ke Nasarawa lokacin da ya ke hanyar zuwa gonarsa.

Wannan labari na zuwa ne mako biyu da sace sarkin Kajuru na Kadunan, Alhaji Alhassan Adamu.

An saki sarkin sa'o'i 24 da sace shi, amma dai iyalansa 13 da aka sace tare da shi har yanzu ba a sake su ba.

Ƴan bindigar sun nemi a biya su kudin fansa har naira miliyan 200.


No comments