'Yan Bindiga Sun Kashe Janar Din Sojan Nijeriya A Abuja

 


Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa an kashe Manjo Janar Hassan Ahmed na rundunar ta su.

Rundunar ta sanar da cewa an kashe Janar Hassan Ahmed ne lokacin da wasu 'yan bindiga suka far wa motarsa a hanyar Lokoja zuwa Abuja a jiya Alhamis.

Wata sanarwa da babban hafsan sojin Laftanar janar Faruk Yahaya ya fitar ta bayyana cewa wata tawagar rundunar sojin ta je yi wa matar marigayin ta'aziyya.

Haka kuma, sanarwar ta ce za a yi wa Janar Faruk jana'iza a makabartar Lungi yau Juma'a da karfe 10 na safe.


Post a Comment

0 Comments