'Yan Bindiga Sun Sace Sama Da Matafiya 50 A Sakkwato

 


Majiyarmu ta BBC ta labarto cewa; akalla matafiya 50 'yan bindiga suka sace a Sokoto, kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayyana.

Jaridar PREMIUM TIMESta ambatocewa wani babban jami'in gwamnati ne ya tabbatar mata da hakan, sai dai bai bayyana mata adadin mutanen da aka sace ba.

Matafiyan suna tafiya ne daga Sokoto zuwa Gusau lokacin da aka sace su a ranar Lahadi.

Ba dai a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba a safiyar ranar Lahadin, amma wadanda suka ga faruwar lamarin sun ce mutanen da aka sace sun kai 50.

Majiyoyi da yawa sun shaida wa kafar yada labaran cewa mafi yawan wadanda aka sacen fasinjojin kamfanin safara ne na Jihar Sokoto da ake kira SPORA.

Amma da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai shugaban kamfanin sufin motoci na Sokoto Yahuza Chika cewa ya yi mota daya ce kawai ta su cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Post a Comment

0 Comments